Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 25:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. domin haka zan miƙa hannuna gāba da ku, zan bashe ku, ku lalace a ƙasashe, zan hallaka ku. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”

8. Ubangiji Allah ya ce, “Da yake Mowab da Seyir sun ce mutanen Yahuza sun zama kamar al'ummai,

9. saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab daga garuruwan da suke kan iyaka, waɗanda su ne darajarta, wato Bet-yeshimot, da Ba'al-meyon, da Kiriyatayim.

10. Zan bashe ta duk da Ammonawa su zama abin mallakar mutanen gabas, don kada um'ƙara tunawa da su a cikin al'ummai.

11. Zan hukunta Mowab, sa'an nan za ta sani ni ne Ubangiji.”

12. Ubangiji Allah ya ce, “Da yake Edom ta ɗaukar wa kanta fansa a kan mutanen Yahuza, ta yi babban laifi da ta ɗaukar wa kanta fansa,

13. domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Edom. Zan kashe mutanenta da dabbobinta, zan maishe ta kufai. Za a kashe su da takobi, tun daga Teman har zuwa Dedan.

14. Mutanen Isra'la za su ɗaukar mini fansa a kan Edom. Za su aukar da fushina da hasalata a kan Edom, sa'an nan Edom za ta san sakayyata, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

15. Ubangiji Allah ya ce, “Tun da yake Filistiyawa sun yi sakayya, sun ɗauki fansa da muguwar zuciya da ƙiyayya marar ƙarewa, don su hallakar,

16. domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Filistiyawa. Zan kashe Keretiyawa, in hallaka sauran mazaunan gāɓar teku.

17. Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na ɗauki fansa a kansu.”

Karanta cikakken babi Ez 25