Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 23:24-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Za su zo daga arewa su yi yaƙi da ke da karusai, da kekunan dawakai, da rundunar mutane. Za su kafa miki sansani a kowace sashi su yi yaƙi da ke da sulke, da garkuwa, da kwalkwali. Zan danƙa shari'a a hannunsu, za su kuwa shara'anta ki da irin shari'arsu.

25. Zan yi fushi da ke don su wulakanta ki. Za su datse hancinki da kunnuwanki. Waɗanda suka rage miki za a kashe su da takobi. Za su kama 'ya'yanki mata da maza, waɗanda suka rage miki kuwa, za a ƙone su da wuta.

26. Za su tsiraita ki, su kuma kwashe lu'ulu'anki.

27. Zan ƙarasa lalatarki da karuwancinki da kika kawo daga ƙasar Masar, don kada ki ƙara ɗaga idonki ki dubi Masarawa, ko ki ƙara tunawa da su.

28. “Gama ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ga shi, zan danƙa ki a hannun waɗanda kike ƙinsu, waɗanda kika ƙi su, kika kuwa rabu da su.

29. Za su nuna miki ƙiyayya, za su ƙwace dukiyarki su bar ki tsirara tik, za su kuma buɗe tsiraicin karuwancinki.

30. Lalatarki da karuwancinki su suka jawo miki wannan, gama kin yi karuwanci da sauran al'umma kika ƙazantar da kanki da gumakansu.

31. Kin bi halin 'yar'uwarki, domin haka zan hukunta ki kamar yadda na hukunta ta.’ ”

32. Ubangiji Allah ya ce,“Za ki sha babban hukuncin da 'yar'uwarki ta sha,Za a yi miki dariya da ba'a,Gama hukuncin yana da tsanani.

33. Za ki sha wahala da baƙin ciki,Hukunci na bantsoro da lalacewa,Shi ne irin hukuncin da aka yi wa 'yarki Samariya.

34. Ƙoƙon da kika sha hukunci daga ciki, za ki lashe shi,Ki tattaune sakainunsa,Ki tsattsage nononki,Ni Ubangiji Allah na faɗa.”

35. Ubangiji ya ce, “Da yake kin manta da ni, kin ba ni baya. Don haka ki ɗauki hakkin lalatarki da karuwancinki.”

36. Sai Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ko ka shara'anta wa Ohola da Oholiba? To, sai ka faɗa musu mugayen ayyukansu.

37. Gama sun yi zina da kisankai, sun bauta wa gumakansu, har ma sun miƙa musu 'ya'yansu maza da suka haifa mini, su zama abincinsu.

38. Ga kuma abin da suka yi mini, sun ƙazantar da Haikalina a ranar, sun kuma ɓata ranar Asabar ɗina.

39. Gama a ranar da suka kashe 'ya'yansu, suka miƙa su hadaya ga gumakansu, sai suka shiga Haikalina suka ƙazantar da shi. Abin da suka yi ke nan cikin Haidalina.

Karanta cikakken babi Ez 23