Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 21:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ya ɗan mutum, ka fuskanci Urushalima, ka yi magana gāba da masujadanta, ka kuma yi annabci a kan ƙasar Isra'ila.

3. Ka faɗa wa ƙasar Isra'ila, ka ce, ni Ubangiji na ce ina gāba da ita. Zan zare takobina daga cikin kubensa, in karkashe adalai da mugaye daga cikinta.

4. Da yake zan karkashe adalai da mugaye daga cikinta, domin haka takobina zai fito daga cikin kubensa, ya karkashe dukan mutane daga Negeb wajen kudu, har zuwa arewa.

5. Dukan mutane kuwa za su sani, ni Ubangiji, na zare takobina daga cikin kubensa, ba kuwa zan sāke mayar da shi a kubensa ba.

6. “Domin haka, ya kai ɗan mutum, sai ka yi nishi, da ajiyar zuciya, da baƙin ciki mai zafi a gabansu.

7. Idan sun tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Saboda labarin abin da yake zuwa. Sa'ad da ya zo, kowace zuciya za ta narke, hannuwa duka za su yi suwu, kowane ruhu kuma zai suma, gwiwoyi duka kuwa za su rasa ƙarfi kamar ruwa. Ga shi, abin yana zuwa, zai tabbata,’ ni Ubangiji Allah na faɗa.”

8. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

9. “Ya ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce ni Ubangiji na ce,‘Takobi, takobi wasasshe,Kuma gogagge!

Karanta cikakken babi Ez 21