Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 4:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai Hatak ya tafi, ya faɗa wa Esta abin da Mordekai ya ce.

10. Esta kuma ta yi magana da Hatak sa'an nan ta aike shi da saƙo a wurin Mordekai cewa,

11. “Dukan barorin sarki da mutanen lardunan sarki sun sani duk wanda ya tafi wurin sarki a shirayi na ciki, ba tare da an kira shi ba, to, doka ɗaya ce take kan mutum, wato kisa, ko mace ko namiji, sai dai wanda sarki ya miƙa wa sandan sarauta na zinariya don ya rayu. Kwana talatin ke nan ba a kira ni in tafi wurin sarki ba.”

12. Hatak ya tafi ya faɗa wa Mordekai abin da Esta ta ce.

13. Sai Mordekai ya ce masa ya je ya faɗa wa Esta haka, “kada ki yi tsammani za ki tsira a fādar sarki fiye da sauran Yahudawa.

14. Gama idan kin yi shiru a irin wannan lokaci, to, taimako da ceto za su zo wa Yahudawa ta wata hanya dabam, amma ke da gidan iyayenki za ku halaka. Wa ya sani ko saboda irin wannan lokaci ne kika sami wannan maƙami?”

15. Sa'an nan Esta ta ce masa ya je ya faɗa wa Mordekai cewa,

16. “Ka tattara dukan Yahudawan da suke a Shushan, su yi domin, kada su ci ko su sha dare da rana, har kwana uku. Ni kuma da kuyangina za mu yi haka nan. Sa'an nan zan tafi wurin sarki, ko da yake ba bisa ga doka ba, idan na halaka, na halaka ke nan.”

17. Sai Mordekai ya tafi ya yi abin da Esta ta umarce shi.

Karanta cikakken babi Esta 4