Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 2:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan waɗannan abubuwa, sa'ad da sarki Ahasurus ya huce daga fushinsa, sai ya tuna da abin da Bashti ta yi, da dokar da aka yi a kanta.

2. Sa'an nan barorin sarki waɗanda suke yi masa hidima suka ce masa, “Bari a samo wa sarki 'yan mata, budurwai, kyawawa.

3. Bari kuma sarki ya sa shugabanni a cikin dukan lardunan mulkinsa su tara dukan kyawawan 'yan mata, budurwai, a gidan matan kulle a masarauta a Shushan, ƙarƙashin Hegai bābā na sarki, wanda yake lura da mata. A riƙa ba budurwan man shafawa.

4. Bari sarki ya zaɓi budurwar da ta gamshe shi, ta zama sarauniya maimakon Bashti.”Sarki fa ya ji daɗin wannan shawara, ya kuwa yi haka ɗin.

5. Akwai wani Bayahude a masarauta a Shushan, mai suna Mordekai ɗan Yayir, ɗan Shimai, ɗan Kish mutumin Biliyaminu.

6. An kamo shi a Urushalima tare 'yan zaman talala waɗanda aka kwashe tare da Yekoniya Sarkin Yahuza, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kai su zaman talala.

7. Mordekai ne ya goyi Hadassa, wato Esta, 'yar kawunsa, gama ita marainiya ce. Ita kuwa kyakkyawa ce. Sa'ad da iyayenta suka rasu, sai Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa.

8. Sa'ad da aka yi shelar dokar sarki, aka kuma tattara 'yan mata a masarauta a Shushan, a hannun Hegai, sai aka ɗauko Esta zuwa fādar sarki, aka sa ta a hannun Hegai wanda yake lura da mata.

9. Esta kuwa ta gamshi Hegai, ta kuma sami farin jini a wurinsa, sai nan da nan ya ba ta man shafawa, da rabon abincinta, da zaɓaɓɓun kuyangi guda bakwai daga fādar sarki. Ya kuma kai ta da kuyanginta a wuri mafi kyau na gidan matan kulle.

10. Esta ba ta riga ta bayyana asalin mutanenta, da danginta ba, gama Mordekai ya umarce ta kada ta yi.

11. Kowace rana Mordekai yakan zo shirayin gidan matan kulle don ya san yadda Esta take.

12. Sa'ad da lokacin kowace budurwa ya yi da za ta shiga wurin sarki Ahasurus, bayan da ta riga ta yi wata goma sha biyu na ka'idar yin kwalliyar mata, wato takan shafe jiki da man ƙanshi wata shida, ta kuma shafe jiki da turare da man shafawa wata shida,

13. sa'an nan budurwar za ta shiga wurin sarki, sai a ba ta dukan abin da take bukata ta ɗauko daga gidan matan kullen zuwa fādar sarki.

14. Takan tafi da yamma, ta koma gidan matan kulle na biyu da safe, a hannun Shawashgaz, bābā na sarki, wanda yake lura da ƙwaraƙwarai. Ba za ta ƙara zuwa wurin sarki ba, sai ko ta sami farin jini a wurin sarki sa'an nan a kirawo ta.

15. Sa'ad da lokacin Esta 'yar Abihail, kawun Mordekai, wadda Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa, ya yi da za ta shiga wurin sarki, ba ta bukaci kome ba, sai dai abin da Hegai, bābā na sarki, wanda yake lura da mata, ya ce. Esta kuwa tana da farin jini a idon duk wanda ya gan ta.

Karanta cikakken babi Esta 2