Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 10:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sarki Ahasurus ya fasa haraji a ƙasar tudu da ta bakin teku.

2. An rubuta a littafin tarihin sarakunan Mediya da na Farisa, dukan ayyukan iko, da isa, da cikakken labarin darajar Mordekai,wadda sarki ya ba shi.

3. Gama sarki Ahasurus kaɗai yake gaba da Mordekai Bayahude, Mordekai kuma yana da girma a wurin Yahudawa, yana kuma da farin jini a wurin taron jama'ar 'yan'uwansa, gama ya nemi lafiyar jama'arsa, yana kuma maganar alheri ga dukan mutane.

Karanta cikakken babi Esta 10