Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 3:6-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.”

7. Don haka da dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta sun ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai suka fāɗi ƙasa, suka yi sujada ga gunkin zinariya wanda sarki Nebukadnezzar ya kafa.

8. A lokacin sai waɗansu Kaldiyawa suka tafi, suka yi ƙarar Yahudawa.

9. Suka ce wa sarki Nebukadnezzar, “Ranka ya daɗe.

10. Kai ne ka yi doka, cewa duk mutumin da ya ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ya fāɗi ƙasa, ya yi sujada ga gunkin zinariya.

11. Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.

12. Akwai waɗansu Yahudawa waɗanda ka naɗa su su lura da harkokin lardin Babila, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Waɗannan mutane fa, ya sarki, ba su kula da kai ba, ba su bauta wa allolinka ba, ba su kuma yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa ba.”

13. Nebukadnezzar fa, ya husata ya umarta a kawo Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Sai aka kawo su gaban sarki.

14. Nebukadnezzar ya ce musu, “Ko gaskiya ne, wai kai Shadrak, da Meshak, da Abed-nego ba ku bauta wa allolina ba, ba ku kuma yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa ba?

15. Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”

16. Shadrak, da Meshak, da Abed-nego kuwa suka amsa wa sarki suka ce, “Ya maigirma Nebukadnezzar, ba mu bukatar mu amsa maka da kome a kan wannan al'amari.

17. Idan haka ne, Allahnmu wanda muke bauta wa, yana da iko ya cece mu daga tanderun gagarumar wuta, zai kuwa kuɓutar da mu daga hannunka, ya sarki.

18. Ko ma bai cece mu ba, ka sani fa ya sarki, ba za mu bauta wa allolinka, ko kuma mu yi wa gunkin zinariya da ka kafa sujada ba.”

Karanta cikakken babi Dan 3