Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 11:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Bayan waɗansu shekaru za su ƙulla zumunci. Sarkin kudu zai aurar wa sarkin arewa da 'yarsa don sāda zumunci, amma ba za ta sami iko ba. Shi da zuriyarsa ba za su amince da ita ba. Za a yi watsi da ita, ita da masu yi mata hidima, da mahaifinta, da waliyyinta.

7. Ba za a daɗe ba, wani daga cikin danginta zai tasar wa sojojin sarkin arewa da yaƙi, ya shiga kagararsu, ya ci su da yaƙi.

8. Zai kwashe gumakansu ganima, da siffofinsu na zubi, ya kai Masar, tare da tasoshinsu na azurfa da na zinariya masu daraja. Zai yi shekaru bai kai wa sarkin arewa yaƙi ba.

9. Bayan wannan sarkin arewa zai kai wa sarkin kudu yaƙi, amma tilas zai janye, ya koma ƙasarsa.

10. “'Ya'yansa maza za su tara babbar rundunar yaƙi. Ɗayansu zai mamaye kamar rigyawa, har ya kai kagara wurin da abokan gāba suke.

11. Sarkin kudu zai husata ya kai wa sarkin arewa yaƙi, za a ba da rundunar sojojin sarkin arewa a hannunsa.

12. Ganin ya kashe sojoji masu ɗumbun yawa, sai ya yi girmankai, amma nasararsa ba mai ɗorewa ba ce.

13. Sarkin arewa kuwa zai tara babbar rundunar soja fiye da ta dā. Bayan waɗansu shekaru kuwa zai kama hanya da babbar rundunar soja, da kayan faɗa masu yawan gaske.

14. “A waɗannan kwanaki mutane da yawa za su tashi gāba da sarkin kudu. Amma waɗansu 'yan kama-karya za su taso daga jama'arka da niyya su cika abin da wahayin ya ce, amma za a fatattaka su.

15. Sa'an nan sarkin arewa zai zo ya gina mahaurai a jikin garun birni don ya ci birnin da yaƙi. Sojojin kudu kuwa ba za su iya tsayawa ba, ko zaɓaɓɓun jarumawansa ma, gama za su rasa ƙarfin tsayawa.

16. Amma wanda ya kawo masa yaƙin zai yi yadda ya ga dama, ba wanda zai iya ja da shi. Zai tsaya a ƙasa mai albarka, ya mallake ta duka.

17. Zai yunƙuro da dukan ƙarfin mulkinsa, zai zo ya gabatar da shawarar salama, ya aikata ta. Zai aurar masa da 'yarsa don ta lalatar da mulkin abokin gabansa, amma wannan dabara ba za ta ci ba.

Karanta cikakken babi Dan 11