Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 10:9-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sa'an nan na ji muryarsa, da jin muryarsa, sai na faɗi rubda ciki, barci mai nauyi ya kwashe ni.

10. Sai hannu ya taɓa ni, ya tashe ni, sa'an nan hannuwana da gwiwoyina suna ta kaɗuwa.

11. Ya ce mini, “Ya Daniyel, mutumin da ake sonka ƙwarai, ka lura da maganar da zan faɗa maka. Ka miƙe tsaye, gama a wurinka aka aiko ni.” Sa'ad da ya faɗi wannan magana, sai na miƙe tsaye, ina rawar jiki.

12. Sai ya ce mini, “Kada ka ji tsoro, Daniyel, gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu'arka, amsar addu'arka ce ta kawo ni.

13. Shugaban ƙasar Farisa ya tare ni har kwana ashirin da ɗaya, amma Mika'ilu, ɗaya daga cikin shugabanni, ya zo ya taimake ni, ya tsaya wurin sarakunan Farisa.

14. Na zo ne don in ganar da kai a kan abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin yana a kan kwanaki na nan gaba ne.”

15. Sa'ad da ya faɗa mini wannan magana, na sunkuyar da kaina ƙasa, na yi shiru, ba magana.

16. Sai wani mai kama da ɗan adam ya taɓa leɓunana, sa'an nan na buɗe baki, na yi magana, na ce wa wanda yake tsaye gabana, “Ya shugabana saboda wannan wahayi ciwo ya kama ni, ba ni da sauran ƙarfi.

17. Ƙaƙa zan iya magana da kai, ya shugabana? Yanzu ba ni da sauran ƙarfi, ba ni kuma da sauran numfashi.”

18. Mai kamannin mutum ɗin nan kuma ya sake taɓa ni, ya kuma ƙarfafa ni.

19. Ya ce, “Ya kai, mutumin da ake sonka ƙwarai, kada ka ji tsoro, salama a gare ka, ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali!”Sa'ad da ya yi magana da ni, na sami ƙarfi na ce, “Yanzu sai shugabana ya yi magana, ka sa na sami ƙarfi.”

20. Shi kuwa ya ce, “Ka san dalilin zuwana wurinka? Yanzu zan koma in yi yaƙi da shugaban Farisa, sa'ad da na murƙushe shi, shugaban Hellas zai taso.

21. Zan faɗa maka abin da yake rubuce a littafin gaskiya. Ba wanda zai taimake ni yaƙi da waɗannan, sai dai Mika'ilu shugabanka.

Karanta cikakken babi Dan 10