Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 1:16-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Don haka baran ya janye shirin ba su abinci da ruwan inabi irin na sarki, ya ci gaba da ba su kayan lambu.

17. Waɗannan samari huɗu kuwa, Allah ya ba su ilimi, da sanin littattafai, da hikima. Ya kuma yi wa Daniyel baiwar ganewar wahayi da mafarkai.

18. Sa'ad da lokacin da sarki ya ƙayyade ya ƙare, sarkin fāda ya gabatar da su a gaban Nebukadnezzar.

19. Da sarki ya yi magana da su, sai ya tarar a cikinsu duka, ba wani kamar Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya. Don haka aka maishe su 'yan majalisar sarki.

20. A cikin dukan abin da ya shafi hikima da ganewa wanda sarki ya nemi shawararsu, sai ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa har sau goma.

21. Daniyel kuwa ya ci gaba har shekarar farko ta sarki Sairas.

Karanta cikakken babi Dan 1