Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 9:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Allah ya rataye taurari a sararin sama,Wato su mafarauci da kare da zomo,Da kaza da 'ya'yanta da taurarin kudu.

10. Ba shi yiwuwa mu gane manyan abubuwa da yake yi.Ayyukan al'ajabansa ba su da iyaka.

11. “Allah yana wucewa kusa da ni,Amma ba na ganinsa.

12. Yakan ɗauki abin da yake so, ba wanda yake hana shi,Ba wanda yake tambayarsa cewa,‘Me kake yi?’

13. “Allah ba zai huce fushinsa ba.Ya murƙushe maƙiyansa waɗanda suka taimaki dodon ruwan nan da ake kira Rahab, wanda ya tayar masa.

14. To, ƙaƙa zan yi in samo kalmomin da zan amsa wa Allah?

15. Ko da yake ba ni da laifi,Duk da haka iyakar abin da zan iya yi ke nan,In roƙi Allah ya yi mini jinƙai,Shi da yake alƙalina.

16. Amma duk da haka ko ya yardar mini in yi magana ma,Ban yi tsammani zai saurare ni ba.

17. Shi ya aiko da hadura, suka yi kacakaca da ni,Suka ƙuƙƙuje ni, ga shi kuwa, ba wani dalilin da ya sa ya yi mini rauni.

Karanta cikakken babi Ayu 9