Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 9:24-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Allah ya ba da duniya ga mugaye,Ya makantar da dukan alƙalai,Idan ba Allah ne ya yi haka nan ba, to, wa ya yi?

25. “Kwanakina suna shuɗewa da sauri, ba mai kyau ko ɗaya.

26. Raina na wucewa kamar jirgin ruwa mafi sauri,Da sauri ƙwarai kamar juhurma ya kai wa zomo sura.

27. Idan an yi murmushi,Ina ƙoƙari in manta da azabata,

28. Sai dukan wahalar da nake sha ta yi ta firgita ni,Na sani Allah ya ɗauke ni mai laifi.

29. Tun da yake Allah ya ɗauka, ni mai laifi ne,To, me zai sa in damu?

30. Ba sabulun da zai iya wanke zunubaina.

31. Allah ya jefa ni a kwatami,Har tufafina ma suna jin kunyata.

32. Da a ce Allah mutum ne,Da sai in mayar masa da magana,Da sai mun je ɗakin shari'a a yanka mana shari'a.

33. Amma ga shi, ba wanda zai shiga tsakaninmu,Ba wanda zai shara'anta tsakanina da Allah.

34. Ka daina hukunta ni, ya Allah!Ka daina razanar da ni.

35. Ba na jin tsoro,Zan yi magana, domin na san zuciyata.”

Karanta cikakken babi Ayu 9