Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 9:15-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ko da yake ba ni da laifi,Duk da haka iyakar abin da zan iya yi ke nan,In roƙi Allah ya yi mini jinƙai,Shi da yake alƙalina.

16. Amma duk da haka ko ya yardar mini in yi magana ma,Ban yi tsammani zai saurare ni ba.

17. Shi ya aiko da hadura, suka yi kacakaca da ni,Suka ƙuƙƙuje ni, ga shi kuwa, ba wani dalilin da ya sa ya yi mini rauni.

18. Ya hana ni in ko shaƙata,Ina jin haushin dukan abin da yake yi mini.

19. In gwada ƙarfi ne?To, a iya gwada wa Allah ƙarfi?In kai shi ƙara ne?Wa zai sa shi ya je?

20. Ni ba ni da laifin kome, amintacce ne ni,A kunne sai a ji kalmomina kamar na marar gaskiya ne.Kowane abu da na fāɗa, kā da ni yake yi.

21. Ba ni da laifin kome, amma ba na ƙara damuwa.Na gaji da rayuwa.

22. Don haka ban damu da kome ba.Da marar laifin da mai laifin duk, Allah zai hallaka mu.

23. Sa'ad da marar laifi ya mutu farat ɗaya,Allah yakan yi dariya.

24. Allah ya ba da duniya ga mugaye,Ya makantar da dukan alƙalai,Idan ba Allah ne ya yi haka nan ba, to, wa ya yi?

25. “Kwanakina suna shuɗewa da sauri, ba mai kyau ko ɗaya.

26. Raina na wucewa kamar jirgin ruwa mafi sauri,Da sauri ƙwarai kamar juhurma ya kai wa zomo sura.

27. Idan an yi murmushi,Ina ƙoƙari in manta da azabata,

Karanta cikakken babi Ayu 9