Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 9:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ayuba ya amsa.

2. “Ai, na taɓa jin waɗannan duka,Amma ta ƙaƙa mutum zai yi jayayya da Allah har ya yi nasara?

3. Ta ƙaƙa za ka iya jayayya da shi?Yana yiwuwa ya yi maka tambayoyi guda dubuWaɗanda ba wanda zai iya ba da amsarsu.

4. Allah mai hikima ne, mai iko,Ba wanda zai iya ja in ja da shi.

5. Yakan kawar da manyan duwatsu farat ɗaya,Ya hallaka su da fushinsa,

6. Allah yakan aiko da girgizar ƙasa, ya girgiza duniya,Yakan jijjiga ginshiƙan da duniya take zaune a kansu.

7. Allah yana da iko ya hana rana fitowa,Ko kuma ya hana taurari haskakawa da dare.

8. Ba wanda ya taimaki Allah shimfiɗa sammai,Wanda yake taka raƙuman ruwan teku, ya kuma kwantar da su.

9. Allah ya rataye taurari a sararin sama,Wato su mafarauci da kare da zomo,Da kaza da 'ya'yanta da taurarin kudu.

10. Ba shi yiwuwa mu gane manyan abubuwa da yake yi.Ayyukan al'ajabansa ba su da iyaka.

11. “Allah yana wucewa kusa da ni,Amma ba na ganinsa.

12. Yakan ɗauki abin da yake so, ba wanda yake hana shi,Ba wanda yake tambayarsa cewa,‘Me kake yi?’

13. “Allah ba zai huce fushinsa ba.Ya murƙushe maƙiyansa waɗanda suka taimaki dodon ruwan nan da ake kira Rahab, wanda ya tayar masa.

Karanta cikakken babi Ayu 9