Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 8:6-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Idan kana da tsarki da aminci, Allah zai taimake ka,Ya maido da iyalin gidanka, ya yi maka sakayya.

7. Duk hasarar dukiyan nan da ka yi, ba kome ba neIn aka gwada da abin da Allah zai ba ka nan gaba.

8. “Ka tsai da zuciyarka a kan hikima irin ta zamanin dā.Ka kuma yi ta yin tunani a kan gaskiyar da kakanninmu suka koya.

9. Kwanakinmu 'yan kaɗan ne kawai,Ba mu san kome ba,Mu inuwa ne kawai a fuskar duniya.

10. Amma ka yarda masu hikima na zamanin dā su koya maka,Ka kasa kunne ga abin da za su faɗa.

11. “Iwa ba ta tsirowa inda ba ruwa,Ba a taɓa samunta a ko'ina ba sai a fadama.

Karanta cikakken babi Ayu 8