Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 8:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. “Iwa ba ta tsirowa inda ba ruwa,Ba a taɓa samunta a ko'ina ba sai a fadama.

12. In ruwan ta ƙafe, ita ce za ta fara bushewa,Tun tana ƙanƙana ba ta isa a yanke a yi amfani da ita ba.

13. Marasa tsoron Allah kamar iwan nan suke,Ba su da sa zuciya muddin sun rabu da Allah.

14. Suna dogara ga silin zare, murjin gizo-gizo.

15. Idan suka jingina ga saƙar gizo-gizo, za ta iya tokare su?Idan sun kama ta, za ta taimake su tsayawa?

16. “Mugaye sukan tsiro kamar ciyayi a hasken rana,Ciyayin da sukan yaɗu su cinye gona duka.

17. Saiwoyinsu sukan nannaɗe duwatsu,Su riƙe kowane dutse da ƙarfi.

18. Amma idan aka tumɓuke su,Ba wanda zai taɓa cewa sun kasance a wurin.

19. Hakika matuƙar murnar da mugaye suke da ita ke nan,Yanzu waɗansu ne za su zo su gāje wurarensu.

20. “Amma daɗai Allah ba zai rabu da amintattu ba,Ba kuwa zai taɓa taimakon mugun mutum ba.

21. Zai sāke barinka ka yi dariya ka ƙyalƙyata kamar dā,Ka kuma yi sowa da murna matuƙa.

22. Amma zai sa maƙiyanka su sha kunya,Za a shafe gidajen mugaye.”

Karanta cikakken babi Ayu 8