Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 7:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Kamar kamen soja na tilas,Haka zaman 'yan adam take,Kamar zaman mai aikin bauta.

2. Kamar bawa ne wanda yake sa zuciya ga inuwa mai sanyi,Kamar ma'aikaci wanda yake sa zuciya ga lokacin biya.

3. Wata da watanni ina ta aikin banza,Kowane dare ɓacin rai yake kawo mini.

4. Sa'ad da na kwanta barci, sai daren ya daɗa tsawoIn yi ta jujjuyawa duk dare, in ƙosa gari ya waye.

5. Jikina cike yake da tsutsotsi,Ƙuraje duka sun rufe shi,Daga miyakuna mugunya tana ta zuba.

6. Kwanakina sun wuce ba sa zuciya,Sun wuce da sauri kamar ƙoshiyar saƙa.

7. “Ka tuna, ya Ubangiji, raina iska ne kawai,Farin cikina ya riga ya ƙare.

8. Kuna ganina yanzu, amma ba za ku sāke ganina ba.Idan kuka neme ni, za ku tarar ba na nan.

9. Kamar girgijen da yake bajewa ya tafi,Haka nan mutum yake mutuwa.

Karanta cikakken babi Ayu 7