Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 41:15-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. An yi gadon bayansa da jerin garkuwoyi ne,An haɗa su daɓa-daɓa kamar an liƙe.

16. Suna haɗe da juna gam,Ko iska ba ta iya ratsa tsakaninsu.

17. Sun manne da juna har ba su rabuwa.

18. Atishawarsa takan walƙata walƙiya,Idanunsa kuma kamar ketowar alfijir.

19. Harsunan wuta kamar jiniya suna fitowa daga bakinsa,Tartsatsin wuta suna ta fitowa.

20. Hayaƙi na fita daga hancinsaKamar tururi daga tukunya mai tafasa,Ko bāgar da ta kama wuta.

21. Numfashinsa yakan kunna gawayi,Harshen wuta yana fita daga bakinsa.

22. A wuyansa ƙarfi yake zaune,Razana tana rausaya a gabansa.

23. Namansa yana ninke, manne da juna,Gama ba ya motsi.

24. Zuciyarsa tana da ƙarfi kamar dutse,Ƙaƙƙarfa kamar dutsen niƙa.

25. Sa'ad da ya miƙe tsaye, ƙarfafa sukan tsorata,Su yi ta tutturmushe juna.

26. Ko an sare shi da takobi,Ko an nashe shi da māshi ko hargi, ko an jefe shi,Ba sa yi masa kome.

Karanta cikakken babi Ayu 41