Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 40:5-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ai, na riga na yi magana sau ɗaya, har ma sau biyu,Ba zan amsa ba, ba zan ƙara cewa kome ba.”

6. Sa'an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba daga cikin guguwa, ya ce,

7. “Tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji,Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.

8. Kai kanka za ka sa mini laifi?Za ka kā da ni don kai ka barata?

9. Kana da ƙarfi kamar na Allah?Kana iya tsawa da murya kamar tasa?

10. “Ka caɓa ado da kwarjini da ɗaukaka,Ka yafa daraja da maƙami.

11. Ka kwararar da rigyawar fushinka,Ka dubi dukan wanda yake alfarma, a wulakance.

12. Ka dubi dukan wanda yake alfarma ka ƙasƙantar da shi,Ka tattake mugaye a inda suke.

13. Dukansu ka binne su a ƙasa,Ka ɗaure fuskokinsu, ka jefa su a lahira.

Karanta cikakken babi Ayu 40