Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 40:15-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. “Ga dorina wanda ni na halicce ta,Kamar yadda na halicce ka,Tana cin ciyawa kamar sa.

16. Ga shi, ƙarfinta yana cikin ƙugunta,Ikonta yana cikin tsakar cikinta.

17. Na yi mata wutsiya miƙaƙƙiya, mai ƙarfi kamar itacen al'ul,Jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe wuri ɗaya

18. Ƙasusuwanta bututun tagulla ne,Gaɓoɓinta kamar sandunan ƙarfe ne.

19. “Ita ce ta farko cikin ayyukan Allah,Sai Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkararta da takobi!

20. Gama duwatsu suke ba ta abinci,A inda dukan namomin jeji suke wasa.

21. Takan kwanta a inuwar ƙaddaji,Ta ɓuya a cikin iwa, da a fadama.

22. Gama inuwar da take rufe ta ta ƙaddaji ce,Itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.

23. Ga shi, ba ta jin tsoron tumbatsar kogi,A natse take, ko da ta bakinta rigyawar Urdun take wucewa.

24. Akwai wanda zai iya kama ta da ƙugiya,Ko ya sa mata asirka?”

Karanta cikakken babi Ayu 40