Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 4:3-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ka koya wa mutane da yawa,Ka kuma ƙarfafa hannuwan marasa ƙarfi.

4. Idan wani ya yi tuntuɓe,Ya gaji, ya rasa ƙarfi,Kalmominka suka ƙarfafa zuciyarsa,Har ya iya tsayawa kyam.

5. Yanzu naka lokacin wahala ya zo,Kai kuwa ka rikice, ka kasa ɗaurewa,

6. Kana yi wa Allah sujada,Ba wani laifi a zamanka,Ya kamata ka amince ka sa zuciya.

7. “Yanzu fa sai ka yi tunani.Ka faɗi bala'i ɗaya wanda ya taɓa fāɗa wa adalin mutum.

8. Na taɓa ganin mutane suna huɗe gonar mugunta,Suna shuka mugunta,Suka kuwa girbe mugunta.

9. A cikin fushinsa Allah yakan hallaka su kamar hadiri.

10. Mugaye sukan yi ruri suna gurnani kamar zakoki,Amma Allah yakan sa su yi tsit,Ya kakkarya haƙoransu.

11. Kamar zakoki da ba su da abin da za su kashe su ci,Haka nan za su mutu, 'ya'yansu kuwa su warwatse duka.

12. “Wata rana wani saƙo ya zo a hankali,Har da ƙyar nake iya ji,

Karanta cikakken babi Ayu 4