Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 4:12-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. “Wata rana wani saƙo ya zo a hankali,Har da ƙyar nake iya ji,

13. Kamar wani irin mafarki mai razanarwa yake,Wanda ya hana ni jin daɗin barcina.

14. Na yi rawar jiki ina makyarkyata,Duk jikina yana ta ɓare-ɓare don tsoro.

15. Wata iska marar ƙarfi ta taɓa fuskata,Sai fatar jikina ta yanƙwane saboda fargaba.

16. Na ga wani abu can yana tsaye,Na zura ido, amma ban san kowane irin abu ba ne,Ina cikin wannan hali sai na ji murya,

17. Ta ce, ‘Mutum yana iya zama adali a gaban Allah?Akwai kuma wanda yake mai tsarki a gaban Mahaliccinsa?

18. Allah ba ya amince wa barorinsa na cikin sammai,Yakan sami laifi a wurin mala'ikunsa.

19. Ta ƙaƙa zai amince da talikinsa wanda aka yi da ƙasa,Abin da yake na ƙura, ana kuwa iya murƙushe shi kamar asu.

20. Mai yiwuwa ne mutum yana raye da safeAmma ya mutu ba a sani ba kafin maraice.

21. Duk abin da ya mallaka an ɗauke,Duk da haka ya mutu cikin rashin hikima.’ ”

Karanta cikakken babi Ayu 4