Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 38:25-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. “Wa ya haƙa hanyar da ruwan sama mai kwararowa zai bi?Da kuma hanyar da gatarin aradu zai bi?

26. Wa ya kuma kawo ruwan sama a ƙasar da ba mutane,Da a cikin hamada inda ba kowa,

27. Don a shayar da zozayar ƙasa inda ba kowa,Har ta tsiro da ciyayi?

28. “Ruwan sama yana da mahaifi?Wa ya haifi ɗiɗɗigar raɓa?

29. Wace ce mahaifiyar ƙanƙara?Wace ce kuma ta haifi jaura?

30. Ruwa ya daskare ya yi ƙarfi kamar dutse,Teku ta daskare.

31. “Za ka iya ɗaure sarƙoƙin kaza-da-'ya'yanta?Ko ka iya kwance igiyoyin mafarauci-da-kare-da-zomo?

32. Za ka iya bi da yaneyanen sararin sama bisa ga fasalinsu?

33. Ka san ka'idodin sammai?Ko ka iya faɗar yadda suka danganta da duniya?

34. “Kana iya yi wa gizagizai tsawa,Don su kwararo ruwan sama, ya rufe ka?

35. Ka iya aikar walƙiyoyi su tafi,Sa'an nan su ce maka, ‘Ga mu mun zo?’

36. Wa ya sa hikima a gizagizai,Ko kuma wa ya ba da ganewa ga kāsashi?

37. Akwai mai hikimar da zai iya ƙidaya gizagizai?Ko kuwa wa zai iya karkato da salkunan ruwan sammai,

38. Sa'ad da ƙura ta murtuke ta taru jingim, ta game kam?

39. “Ka iya farauto wa zakoki abinci?Ko ka ƙosar da yunwar sagarun zakoki,

40. Sa'ad da suke fako a kogwanninsu,Ko suna kwance suna jira a maɓoyarsu?

41. Wa yake tanada wa hankaka abincinsa,Sa'ad da 'ya'yansa suke kuka ga Allah,Suna kai da kawowa saboda rashin abinci?”

Karanta cikakken babi Ayu 38