Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 36:8-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma idan aka ɗaure su da sarƙoƙi,Da kuma igiyar wahala,

9. Sa'an nan yakan sanar da su aikinsuDa laifofin da suke yi na ganganci.

10. Yakan sa su saurari koyarwa,Da umarnai, cewa su juya, su bar mugunta.

11. Idan suka kasa kunne suka bauta masa,Za su cika kwanakinsu da wadata,Shekarunsu kuma da jin daɗi.

12. Amma idan ba su kasa kunne ba,Za a hallaka su da takobi,Su mutu jahilai.

13. “Waɗanda ba su da tsoron Allah a zuciyarsu,Suna tanada wa kansu fushi,Ba su neman taimako sa'ad da ya ɗaure su.

14. Sukan yi mutuwar ƙuruciya,Sukan ƙare kwanakinsu da kunya.

15. Zai kuɓutar da waɗanda suke shan tsanani,Ta wurin tsananin da suke sha,Yakan buɗe kunnuwansu ta wurin shan wahala.

16. Allah ya tsamo ka daga cikin wahala,Ya kawo ka yalwataccen wuri inda ba matsi,Abincin da aka yi na addaras aka jera maka a kan tebur.

17. “Ka damu ƙwarai don ka ga an hukunta mugaye,Amma hukunci da adalci sun kama ka.

Karanta cikakken babi Ayu 36