27. “Allah yakan sa ruwa ya zama tururi,Ya maishe shi ruwan sama,
28. Wanda yakan kwararo daga sama,Ya zubo wa ɗan adam a yalwace.
29. Wa zai iya gane yadda gizagizai suke shimfiɗe a sararin sama,Da tsawar da ake yi a cikinsu?
30. Ga shi, yakan baza waƙiya kewaye da shi,Yakan rufe ƙwanƙolin duwatsu.Zurfin teku yana nan da duhunsa.
31. Gama ta haka yakan shara'anta mutane,Yakan ba da abinci a yalwace.
32. Ya cika hannunsa da walƙiya,Yakan sa ta faɗa a kan abin da ya bārata.
33. Tsawarta tana nuna kasancewar Allah,Ko shanu sun san da zuwan hadiri.”