Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 36:24-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. “Ka tuna ka girmama aikinsa,Wanda mutane suke yabo.

25. Dukan mutane sun ga ayyukansa,Sun hango shi daga nesa.

26. Ga shi kuwa, Allah Maɗaukaki ne,Ba mu kuwa san iyakar ɗaukakarsa ba,Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.

27. “Allah yakan sa ruwa ya zama tururi,Ya maishe shi ruwan sama,

28. Wanda yakan kwararo daga sama,Ya zubo wa ɗan adam a yalwace.

29. Wa zai iya gane yadda gizagizai suke shimfiɗe a sararin sama,Da tsawar da ake yi a cikinsu?

30. Ga shi, yakan baza waƙiya kewaye da shi,Yakan rufe ƙwanƙolin duwatsu.Zurfin teku yana nan da duhunsa.

31. Gama ta haka yakan shara'anta mutane,Yakan ba da abinci a yalwace.

32. Ya cika hannunsa da walƙiya,Yakan sa ta faɗa a kan abin da ya bārata.

33. Tsawarta tana nuna kasancewar Allah,Ko shanu sun san da zuwan hadiri.”

Karanta cikakken babi Ayu 36