Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 36:19-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Kukanka ya iya raba ka da wahala,Ko kuwa dukan ƙarfin da kake da shi?

20. Kada ka ƙosa dare ya yi,Domin a lokacin nan ne mutane sukan watse,Kowa ya kama gabansa.

21. Ka lura kada ka rinjayu a kan aikata mugunta,Gama saboda haka kake shan wannan tsanani,Don a tsare ka daga aikata mugunta.

22. “Duba, Allah Maɗaukaki ne cikin ikonsa,Wa ya iya koyarwa kamarsa?

23. Ba wanda zai iya tsara wa Allah abin da zai yi,Wa ya isa ya ce masa ya yi kuskure?

24. “Ka tuna ka girmama aikinsa,Wanda mutane suke yabo.

25. Dukan mutane sun ga ayyukansa,Sun hango shi daga nesa.

26. Ga shi kuwa, Allah Maɗaukaki ne,Ba mu kuwa san iyakar ɗaukakarsa ba,Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.

27. “Allah yakan sa ruwa ya zama tururi,Ya maishe shi ruwan sama,

28. Wanda yakan kwararo daga sama,Ya zubo wa ɗan adam a yalwace.

29. Wa zai iya gane yadda gizagizai suke shimfiɗe a sararin sama,Da tsawar da ake yi a cikinsu?

Karanta cikakken babi Ayu 36