Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 36:15-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Zai kuɓutar da waɗanda suke shan tsanani,Ta wurin tsananin da suke sha,Yakan buɗe kunnuwansu ta wurin shan wahala.

16. Allah ya tsamo ka daga cikin wahala,Ya kawo ka yalwataccen wuri inda ba matsi,Abincin da aka yi na addaras aka jera maka a kan tebur.

17. “Ka damu ƙwarai don ka ga an hukunta mugaye,Amma hukunci da adalci sun kama ka.

18. Ka lura kada ka bar hasalarka ta sa ka raina Allah,Kada kuma ka bar wahalar da kake sha ta sa ka ɓata da mai fansarka.

19. Kukanka ya iya raba ka da wahala,Ko kuwa dukan ƙarfin da kake da shi?

20. Kada ka ƙosa dare ya yi,Domin a lokacin nan ne mutane sukan watse,Kowa ya kama gabansa.

21. Ka lura kada ka rinjayu a kan aikata mugunta,Gama saboda haka kake shan wannan tsanani,Don a tsare ka daga aikata mugunta.

22. “Duba, Allah Maɗaukaki ne cikin ikonsa,Wa ya iya koyarwa kamarsa?

Karanta cikakken babi Ayu 36