Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 35:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Elihu kuwa ya yi magana.

2. “Ayuba, ba daidai ba ne, ka ce,Ba ka yi laifi a gaban Allah ba,

3. Ka kuwa ce, ‘Wace riba na ci?Wane fifiko nake da shi fiye da idan na yi zunubi?’

4. Zan ba ka amsa, kai da abokanka.

5. Ka duba sama,Ka dubi gizagizai waɗanda suke can sama da kai.

6. Idan ka yi zunubi, da me ka cuci Allah?Idan ka aikata laifofi da yawa, wace cuta ka yi masa?

7. Idan kai adali ne da me ka ƙara masa,Ko kuwa me ya samu daga gare ka?

Karanta cikakken babi Ayu 35