Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 34:24-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Yakan ragargaza ƙarfafa ba tare da wani bincike ba,Ya sa waɗansu a madadinsu.

25. Saboda sanin ayyukansu,Yakan kaɓantar da su da dare ya ragargaza su,

26. Yakan buge su a gaban mutane saboda muguntarsu,

27. Don sun daina binsa, ba su kula da ko ɗayaDaga cikin umarnansa ba.

28. Suka sa matalauta su yi kuka ga Allah,Ya kuwa ji kukan waɗanda ake tsananta wa.

29. Idan Allah zai yi shiru, da wa zai sa wa wani laifi?Idan ya ɓoye fuskarsa, wa zai iya ganinsa,Ko aka yi wa al'umma ko ga mutum?

30. Bai kamata marar tsoron Allah ya yi mulki ba,Don kada ya tura jama'a cikin tarko.

31. “Akwai wanda zai ce wa Allah, ‘Ni horarre ne,Ba zan ƙara yin laifi ba?

32. Ka koya mini abin da ban sani ba,Idan na yi laifi, ba zan ƙara yi ba.’

33. Zai kuɓutar domin ya gamshe ka saboda ka ƙi yarda?Tilas kai za ka zaɓa, ba ni ba,Saboda haka sai ka hurta abin da ka sani.

34. “Haziƙan mutane da mutum mai hikima da suka ji ni za su ce,

35. ‘Ayuba yakan yi magana ne ba tare da sanin abin da yake yi ba,Maganarsa ba ta mai hangen nesa ba ce.

36. Da ma a gwada Ayuba har ƙarshe,Saboda amsar da yake bayarwa ta mugaye.

37. Gama ya ƙara zunubinsa da tayarwa,Yana tafa hannunsa a tsakaninmu,Yana yawaita maganganunsa gāba da Allah.’ ”

Karanta cikakken babi Ayu 34