Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 34:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Elihu ya ci gaba.

2. “Ku mutane masu hikima, ku ji maganata,Ku kasa kunne ga abin da zan faɗa, ku masana.

3. Kunne yake rarrabewa da magana,Kamar yadda harshe yake rarrabewa da ɗanɗanar abinci.

4. Bari mu zaɓi abin da yake daidai,Bari kuma mu daidaita abin da yake mai kyau tsakanin junanmu.

5. Gama Ayuba ya ce, ‘Ni marar laifi ne,Amma Allah ya ƙwace mini halaliyata.

6. Duk da rashin laifina an ɗauke ni a maƙaryaci,Raunina ba ya warkuwa ko da yake ba ni da laifin kome.’

Karanta cikakken babi Ayu 34