Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 33:23-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. “Da a ce akwai wani mala'ika mai sulhuntawa a tsakani,Ko da ɗaya daga cikin dubu ne wanda zai faɗa wa mutum,

24. Mala'ikan da zai yi masa alheri ya ce,‘Ka cece shi daga gangarawa zuwa cikin kabari,Na sami abin da zai fanshe shi!’

25. Naman jikinsa zai koma kamar na saurayi,Zai komo kamar lokacin da yake gaɓar ƙarfinsa.

26. Sa'an nan ne mutum zai yi addu'a ga Allah, ya karɓe shi,Ya zo gabansa da murna,Allah zai komar wa mutum da adalcinsa.

27. Zai raira waƙa a gaban jama'a, ya ce, ‘Na yi zunubi. Ban yi daidai ba,Amma ba a sa ni in biya ba.

28. Allah ya fanshe ni daga gangarawa zuwa kabari,Raina kuwa zai ga haske.’

29. “Ga shi kuwa, Allah ya yi dukan waɗannan abubuwa sau biyu, har ma sau uku ga mutum,

30. Don ya komo da ran mutum daga kabari,Domin a haskaka shi da hasken rai.

31. “Haba Ayuba, ka kula fa, ka kasa kunne,Ga abin da nake faɗa,Ka yi shiru, zan yi magana.

32. Amma idan kana da ta cewa, to, amsa,Yi magana, gama ina so in kuɓutar da kai.

33. In kuwa ba haka ba, sai ka yi shiru,Ka kasa kunne gare ni,Zan kuwa koya maka hikima.”

Karanta cikakken babi Ayu 33