Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 33:15-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Yakan sanar a mafarkai ko a wahayiSa'ad da barci mai nauyi ya ɗauke su,A sa'ad da suke barci a gadajensu.

16. Yakan buɗe kunnuwan mutane,Ya tsorata su da faɗakarwarsa,

17. Domin ya kawar da su daga aikin da suke yi,Ya kuma kawar musu da girmankai.

18. Yakan hana su zuwa kabari,Ya hana ransu halaka da takobi.

19. “Akan hori mutum da cuta mai zafi a gadonsa,Ya yi ta fama da azaba a cikin ƙasusuwansa,

20. Ransa yana ƙyamar abinci,Yana ƙyamarsa kome daɗinsa kuwa.

21. Yakan rame ƙangayau, ƙasusuwansa duk a waje.

22. Yana gab da shiga kabari,Ransa yana hannun mala'ikun mutuwa.

23. “Da a ce akwai wani mala'ika mai sulhuntawa a tsakani,Ko da ɗaya daga cikin dubu ne wanda zai faɗa wa mutum,

24. Mala'ikan da zai yi masa alheri ya ce,‘Ka cece shi daga gangarawa zuwa cikin kabari,Na sami abin da zai fanshe shi!’

25. Naman jikinsa zai koma kamar na saurayi,Zai komo kamar lokacin da yake gaɓar ƙarfinsa.

Karanta cikakken babi Ayu 33