Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 33:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ya saka ka a turu,Yana duban dukan al'amuranka.

12. “Amma a kan wannan, Ayuba, ka yi kuskure, zan ba ka amsa,Gama Allah ya fi kowane mutum girma.

13. Me ya sa kake yi wa Allah gunaguni,Cewa ba ya karɓar maganarka ko ɗaya?

14. Gama Allah yakan yi magana sau ɗaya ne,I, har sau biyu, duk da haka mutum ba ya lura.

15. Yakan sanar a mafarkai ko a wahayiSa'ad da barci mai nauyi ya ɗauke su,A sa'ad da suke barci a gadajensu.

16. Yakan buɗe kunnuwan mutane,Ya tsorata su da faɗakarwarsa,

17. Domin ya kawar da su daga aikin da suke yi,Ya kuma kawar musu da girmankai.

18. Yakan hana su zuwa kabari,Ya hana ransu halaka da takobi.

19. “Akan hori mutum da cuta mai zafi a gadonsa,Ya yi ta fama da azaba a cikin ƙasusuwansa,

20. Ransa yana ƙyamar abinci,Yana ƙyamarsa kome daɗinsa kuwa.

21. Yakan rame ƙangayau, ƙasusuwansa duk a waje.

22. Yana gab da shiga kabari,Ransa yana hannun mala'ikun mutuwa.

Karanta cikakken babi Ayu 33