Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 33:1-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Amma yanzu, kai Ayuba, ka yarda ka ji maganata,Ka kasa kunne ga dukan abin da zan faɗa.

2. Ga shi, na buɗe baki in yi magana.

3. Maganar da zan hurta ainihin gaskiyar da take a zuciyata ce,Abin da zan faɗa kuma dahir ne.

4. Ruhun Allah ne ya yi ni, Mai Iko Dukka ya hura mini rai.

5. “Ka amsa mini, in ka iya,Ka shirya abubuwan da za ka faɗa mini, ka yi tsaye a kansu.

6. Duba, ni da kai ɗaya muke a wajen Allah,Dukanmu biyu kuma daga yumɓu aka siffata mu.

7. Don haka kada ka razana saboda ni,Abin da zan faɗa maka, ba abin da zai fi ƙarfinka.

8. “Hakika na ji maganar da ka yi,Na kuwa ji amon maganganunka,

9. Ka ce kai tsattsarka ne, ba ka da laifi,Kai tsabtatacce ne, ba ka da wata ƙazanta.

10. Ka ce Allah ya zarge ka ya ɗauke ka tankar maƙiyansa,

11. Ya saka ka a turu,Yana duban dukan al'amuranka.

12. “Amma a kan wannan, Ayuba, ka yi kuskure, zan ba ka amsa,Gama Allah ya fi kowane mutum girma.

13. Me ya sa kake yi wa Allah gunaguni,Cewa ba ya karɓar maganarka ko ɗaya?

14. Gama Allah yakan yi magana sau ɗaya ne,I, har sau biyu, duk da haka mutum ba ya lura.

15. Yakan sanar a mafarkai ko a wahayiSa'ad da barci mai nauyi ya ɗauke su,A sa'ad da suke barci a gadajensu.

16. Yakan buɗe kunnuwan mutane,Ya tsorata su da faɗakarwarsa,

17. Domin ya kawar da su daga aikin da suke yi,Ya kuma kawar musu da girmankai.

Karanta cikakken babi Ayu 33