Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 32:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. “Ga shi, na dakata na ji maganarku,Na kasa kunne ga maganarku ta hikima,Tun kuna tunani a kan abin da za ku faɗa.

12. Na kasa kunne gare ku sosai,Amma ko ɗaya ba wanda ya kā da Ayuba.Ba kuma wanda ya ba shi amsar tambayarsa.

13. Ku lura kada ku ce kuna da hikima,Allah ne kaɗai yake da iko ya kā da shi, ba mutum ba.

14. Ba da ni Ayuba yake magana ba,Saboda haka ba zan amsa masa da irin amsarku ba.

15. “Abin ya cika musu ciki, ba su ƙara amsawa ba,Wato ba su da ta cewa.

16. Ni kuma sai in tsaya don ba su ce kome ba?Sun tsaya kurum, don ba su da ta cewa?

17. A'a, ni kuma zan ba da tawa amsa,In kuma faɗi ra'ayina.

18. Cike nake da magana,Ruhun da ka cikina ya iza ni.

19. Ga zuciya tana kama da ruwan inabin da ba shi da mafitar iska,Kamar sabuwar salkar ruwan inabi wadda take shirin fashewa.

20. Tilas in yi magana don in huce,Dole in ba da amsa.

21. Ba zan yi wa kowa son zuciya ba,Ko kuma in yi wa wani fādanci.

22. Gama ni ban iya fādanci ba,Idan na yi haka kuwaMahaliccina zai kashe ni nan da nan.”

Karanta cikakken babi Ayu 32