Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 32:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Mutanen nan uku sun daina ba Ayuba amsa, saboda yana ganin kansa adali ne.

2. Sai Elihu, ɗan Barakel, mutumin Buz, daga cikin iyalin Arama, ya husata, yana fushi da Ayuba saboda ya baratar da kansa, bai bari Allah ya baratar da shi ba.

3. Yana kuma fushi da abokan nan uku na Ayuba, domin sun rasa amsar da za su ba Ayuba, ko da yake sun hurta Ayuba ne yake da laifi.

4. Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka.

5. Sa'ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da wata amsa da za su ba Ayuba, sai ya yi fushi.

6. Elihu ɗan Barakel, mutumin Buz, ya fara magana, ya ce,“A shekaru dai ni yaro ne ku kuwa manya ne,Don haka ina jin nauyi,Ina kuma jin tsoro in faɗa muku ra'ayina.

7. Na ce wa kaina, ‘Ya kamata kwanaki su yi magana,Yawan shekaru kuma su koyar da hikima.’

8. Amma Ruhun Allah Mai Iko Dukka ne wanda yake cikin mutum,Yakan ba mutane basira.

9. Ba tsofaffi ne masu wayo ba,Ba kuma masu yawan shekaru kaɗai yake gane abin da yake daidai ba.

10. Don haka na ce ku kasa kunne gare ni,Bari in faɗa muku nawa ra'ayi.

Karanta cikakken babi Ayu 32