Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 31:24-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. “Idan na ce ga zinariya na dogara, ko zinariya tsantsa ita ce jigona,

25. Idan kuma saboda yawan dukiyata nake fariya,Ko saboda abin da na mallaka ne,

26. Idan ga hasken rana nake zuba ido,Ko ga hasken farin wata ne,

27. Zuciyata ta jarabtu ke nan a asirce,Ni da kaina ina sumbatar hannuna,

28. Wannan ma zai zama laifi ne wanda alƙalai za su hukunta,Gama na zama munafukin Allah Mai Iko Dukka ke nan.

29. “Idan na yi murna saboda wahala ta sami maƙiyana,Ko na yi fariya saboda mugun abu ya same shi,

30. Ban yi zunubi da bakina ba,Ban nemi ran wani ta wurin la'anta shi ba.

31. Ko mutanen da suke cikin alfarwata ba wanda zai ce,Ga wani can da bai ƙoshi da nama ba.

32. Ban bar baƙi su kwana a titi ba,Ƙofar gidana a buɗe take ga matafiya.

33. Idan na ɓoye laifofina a zuciyata,

34. Ko na tsaya shiru saboda tsoron taron jama'a,Saboda kuma baƙar maganar mutane ta razanar da ni,

35. Da a ce ina da wanda zai kasa kunne gare ni,Da sai in sa hannu a kan abin da na faɗa,Allah kuwa Mai Iko Dukka ya amsa mini.“Da ƙarar da maƙiyana suke kai ni, a rubuce ne,

36. Hakika da sai in ɗauke ta a kafaɗata,In kuwa naɗa ta a kaina kamar rawani.

37. Da na ba Allah dukan lissafin abin da na taɓa yi,In tinƙare shi kamar ni basarauce ne.

38. “Idan ƙasata tana kuka da ni,Ita da kunyoyinta,

39. Ko na ci amfaninta ban biya ba,Ko na yi sanadin mutuwar mai ita,

Karanta cikakken babi Ayu 31