Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 31:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Na yi alkawari da idanuna,Me zai sa in ƙyafaci budurwa?

2. Wane rabo zan samu daga wurin Allah a Sama?Wane gādo kuma zan samu daga wurin Mai Iko Dukka a can samaniya?

3. Yakan aika da masifa da lalacewaGa waɗanda suke aikata abin da ba daidai ba.

4. Allah ya san dukan abin da nake yi,Yana ƙididdige dukan takawata.

5. “Idan ina tafiya da rashin gaskiya,Ina hanzari don in aikata yaudara,

6. Bari Allah ya auna ni da ma'aunin da yake daidai,Zai kuwa san mutuncina.

7. Idan dai na kauce daga hanya,Ko kuwa zuciyata ta bi sha'awar idanuna,Idan akwai ko ɗan sofane a hannuna,

8. To, bari in shuka, wani ya ci amfanin,Bari a tumɓuke amfanin gonata.

9. “Idan na yi sha'awar wata mace,Har na je na laɓe a ƙofar maƙwabcina,

Karanta cikakken babi Ayu 31