Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 3:12-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Me ma ya sa uwata ta rungume ni a ƙirjinta,Ta shayar da ni kuma da mamanta?

13. Da a ce na mutu a lokacin, da yanzu ina huce,

14. Da ina ta barcina kamar sarakuna da masu mulkiWaɗanda suka sāke gina fādodi na dā,

15. Da ina ta sharar barcina kamar shugabanniWaɗanda suka cika gidajensu da zinariya da azurfa,

16. In yi ta sharar barci kamar jariran da aka haifa matattu.

17. Mugaye za su daina muguntarsu a kabari,Ma'aikatan da suka gaji da aiki su ma za su huta,

18. Har 'yan sarƙa ma za su ji daɗin salama,Su huta daga tsautawa da umarnai masu tsanani.

19. Kowa da kowa yana wurin, babba da ƙarami duk ɗaya ne,Bayi ma sun sami 'yanci.

20. “Me ya sa ake barin mutane su yi ta zama cikin damuwa?Me ya sa ake ba da haske ga waɗanda suke baƙin ciki?

21. Sun jira mutuwa, amma ta ƙi samuwa,Sun fi son kabari da kowace irin dukiya.

Karanta cikakken babi Ayu 3