Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 3:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ayuba ya yi magana ya la'anci ranar da aka haife shi.

2. Ya ce,“Ya Ubangiji, ka la'anci ranan nan da aka haife ni.

3. Ka la'anci daren nan da aka yi cikina.

4. Ka mai da ranan nan ta zama duhu, ya Allah.Kada a ƙara tunawa da wannan rana,Kada haske ya ƙara haskakata.

5. Ka sa ta zama ranar duhu baƙi ƙirin.Ka rufe ta da gizagizai, kada hasken rana ya haskaka ta.

6. Ka shafe wannan dare daga cikin shekara,Kada kuma a ƙara lasafta shi.

7. Ka sa daren ya zama marar amfani, daren baƙin ciki.

Karanta cikakken babi Ayu 3