Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 27:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ayuba ya amsa.

2. “Na rantse da Allah Mai Iko Dukka,Wanda ya ƙwace mini halaliyata,Wanda ya ɓata mini rai.

3. Muddin ina numfashi,Ruhun Allah kuma yana cikin hancina

4. Bakina ba zai faɗi ƙarya ba,Harshena kuma ba zai hurta maganganun yaudara ba.

5. Allah ya sawwaƙa in ce kun yi daidai,Har in mutu ba zan daina tsare mutuncina ba.

6. Ina riƙe da adalci kam, ba kuwa zan sake shi ba,Zuciyata ba ta zarge ko ɗaya daga cikin kwanakin raina ba.

7. “Bari maƙiyina ya zama kamar mugun mutum,Wanda ya tashi gāba da ni ya zama kamar marar adalci.

8. Wace sa zuciya take ga marar tsoron Allah?Sa'ad da Allah ya datse shi, ya ɗauke ransa?

9. Allah kuwa zai ji kukansa sa'ad da wahala ta same shi?

10. Ko Mai Iko Dukka zai zama abin farin ciki a gare shi?Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?

11. “Zan koya muku zancen ikon Allah,Abin da yake na wajen Mai Iko Dukka ba zan ɓoye ba.

12. Ga shi kuwa, dukanku kun gani da kanku,Me ya sa kuka zama wawaye?

Karanta cikakken babi Ayu 27