Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 26:7-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Allah ne ya shimfiɗa arewa a sarari kurum,Ya rataya duniya ba bisa kan kome ba.

8. Allah ne ya cika gizagizai masu duhu da ruwa,Girgijen kuwa bai kece ba.

9. Ya rufe kursiyinsa, ya shimfiɗa girgije a kansa.

10. Ya shata da'ira a kan fuskar teku,A kan iyakar da take tsakanin haske da duhu.

11. Ginshiƙan samaniya sun girgiza,Sun firgita saboda tsautawarsa.

12. Ta wurin ƙarfinsa ya kwantar da teku,Da saninsa ya hallaka dodon ruwan nan, wato Rahab.

13. Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi garau,Ikonsa ne kuma ya sha zarar macijin nan mai gudu.

Karanta cikakken babi Ayu 26