Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 20:11-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ko da yake gagau yake, ma'aikaci ne kuma sa'ad da yake yaro,Duk da haka ba da jimawa ba, zai zama ƙura.

12-13. Ɗanɗana mugunta yana da daɗi a gare shi ƙwarai,Yakan sa wata a bakinsa don ya riƙa jin daɗin tsotsanta.

14. Amma a cikinsa wannan abinci yakan zama da ɗaci,Ɗacinsa kamar na kowane irin dafi mai ɗaci ne.

15. Mugun mutum yakan harar da dukiyar da ya samu ta hanyar zamba,Allah zai karɓe ta har da wadda ya ci a cikin cikinsa.

16. Abin da mugu ya haɗiye kamar dafi yake,Yakan kashe shi kamar saran maciji mai mugu dafi.

17. Zai mutu bai ga kogunan man zaitun ba,Ba kuwa zai ga rafuffukan da suke da yalwar albarka ba.

18. Tilas ya rabu da dukan abin da ya yi wahalarsa.Ba dama ya mori dukiyarsa,

19. Saboda zalunci da rashin kula da matalauta,Da ƙwace gidajen da waɗansu suka gina.

20. “Har abada ba zai kai ga samun abin da yake wahala ba.

21. Sa'ad da ya ci ba zai yi saura ba,Gama yanzu dukiyarsa ta ƙare.

Karanta cikakken babi Ayu 20