Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 20:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Zofar ya amsa.

2. “Ayuba, ka ɓata mini rai,Ba zan yi haƙuri ba, sai na ba ka amsa.

3. Abin da ka faɗa raini ne,Amma na san yadda zan ba ka amsa.

4. “Hakika ka sani tun daga zamanin dā,Sa'ad da aka fara sa mutum a duniya,

5. Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.

6. Mai yiwuwa ne ya ƙasaita, ya zama kamar hasumiya a sararin sama.Ya ƙasaita har kansa ya taɓa gizagizai.

7. Amma zai shuɗe kamar ƙura.Waɗanda dā suka san shi,Za su yi mamaki saboda rashin sanin inda ya tafi.

8. Zai ɓace kamar mafarki, kamar wahayi da dad dare,Ba kuwa za a ƙara ganinsa ba.

9. Ba za a ƙara ganinsa a wurin zamansa ba.

10. Tilas 'ya'yansa maza su biya zambar da ya yi wa matalauta,Tilas hannuwansa su biya dukiyar da ya ƙwace.

Karanta cikakken babi Ayu 20