Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 2:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da ranar da talikan sama masu rai sukan hallara gaban Ubangiji ta sāke yi, Shaiɗan shi ma ya zo tare da su.

2. Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Ina ka fito?”Sai Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Ina ta kaiwa da kawowa ne, ko'ina a duniya.”

3. Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta. Kai ka sa na yardar maka ka far masa, ba tare da wani dalili ba. Amma duk da haka Ayuba yana nan da amincinsa kamar yadda yake.”

4. Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Mutum ya iya rabuwa da dukan abin da yake da shi don yă ceci ransa.

5. Amma yanzu da a ce za ka taɓa lafiyar jikinsa, da sai yă fito fili yă zage ka.”

6. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Shi ke nan, yana cikin ikonka, amma fa, kada ka kashe shi.”

7. Sa'an nan Shaiɗan ya rabu da Ubangiji, ya je ya sa ƙuraje su fito ko'ina a jikin Ayuba.

Karanta cikakken babi Ayu 2