Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 19:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Gama ya kwashe dukiyata duka,Ya ɓata mini suna.

10. Ya mammangare ni,Ya tumɓuke sa zuciyata,Ya bar ni in yi yaushi, in mutu.

11. Allah ya zaburo mini da fushi,Ya maishe ni kamar mafi mugunta daga cikin maƙiyansa.

12. Ya aiko da rundunar sojansa don ta fāɗa mini,Suka haƙa ramummuka kewaye da alfarwata inda za su yi kwanto.

13. “'Yan'uwana sun yashe ni,Na zama baƙo ga idon sanina.

14. Dangina da abokaina sun tafi.

15. Waɗanda sukan ziyarce gidana sun manta da ni.Barorina mata na gidana sun maishe ni kamar baƙo daga wata ƙasa.

16. Sa'ad da na kira barana, ba ya amsawa,Ko a lokacin da na roƙe shi ya taimake ni.

17. Har matata ma ba ta iya jurewa da ɗoyin numfashina,'Yan'uwana maza kuwa ba su ko zuwa kusa da ni.

Karanta cikakken babi Ayu 19