Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 19:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. A kowane lokaci kuna wulakanta ni,Ba kwa jin kunya yadda kuke zagina.

4. Da a ce ma na aikata abin da yake ba daidai ba ne,Da me ya cuce ku?

5. Tsammani kuke kun fi ni ne,Kuna É—auka cewa wahalar da nake shaTa tabbatar ni mai laifi ne.

6. Ba ku iya ganin abin da Allah ya yi mini,Ya kafa tarko don ya kama ni.

7. Na ce ban yarda da kama-karyarsa ba,Amma ba wanda ya kasa kunne.Na nema a aikata gaskiya, amma sam, babu.

8. Allah ya rufe hanya, na kasa wucewa,Ya rufe hanyata da duhu,

Karanta cikakken babi Ayu 19