Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 19:21-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Ku abokaina ne! Ku ji tausayina!Ikon Allah ya fyaɗa ni ƙasa.

22. Me ya sa kuke ɓata mini rai kamar yadda Allah ya yi?Azabar da kuka yi mini har yanzu ba ta isa ba?

23. “Da ma a ce wani zai rubuta abin da nake faɗa,Ya rubuta shi a littafi!

24. Ko kuwa ya zana kalmomina da kurfi a kan dutse,Ya rubuta su don su tabbata har abada!

25. Amma na sani akwai wani a SamaniyaWanda a ƙarshe zai zo ya tsaya mini.

26. Ko da yake ciwo ya riga ya cinye fatata,A wannan jiki zan ga Allah.

27. Zan gan shi ido da ido,Ba kuwa zai zama baƙo a gare ni ba.“Zuciyata ta karai saboda ku mutane kun ce,

28. ‘Ta ƙaƙa za mu yi masa azaba?’Kuna neman sanadin da za ku fāɗa mini.

29. Amma yanzu, sai ku ji tsoron takobi,Ku ji tsoron takobin da yake kawo hasalar Allah a kan zunubi.Don haka za ku sani akwai wani mai yin shari'a.”

Karanta cikakken babi Ayu 19