Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 19:15-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Waɗanda sukan ziyarce gidana sun manta da ni.Barorina mata na gidana sun maishe ni kamar baƙo daga wata ƙasa.

16. Sa'ad da na kira barana, ba ya amsawa,Ko a lokacin da na roƙe shi ya taimake ni.

17. Har matata ma ba ta iya jurewa da ɗoyin numfashina,'Yan'uwana maza kuwa ba su ko zuwa kusa da ni.

18. 'Yan yara sukan raina ni su yi mini dariya sa'ad da suka gan ni.

19. Aminaina na kusa sukan dube ni, duban ƙyama,Waɗanda na fi ƙaunarsu duka sun zama maƙiyana.

20. Fatar jikina ta saki, ba ƙarfi,Da ƙyar na kuɓuta.

21. Ku abokaina ne! Ku ji tausayina!Ikon Allah ya fyaɗa ni ƙasa.

22. Me ya sa kuke ɓata mini rai kamar yadda Allah ya yi?Azabar da kuka yi mini har yanzu ba ta isa ba?

23. “Da ma a ce wani zai rubuta abin da nake faɗa,Ya rubuta shi a littafi!

24. Ko kuwa ya zana kalmomina da kurfi a kan dutse,Ya rubuta su don su tabbata har abada!

25. Amma na sani akwai wani a SamaniyaWanda a ƙarshe zai zo ya tsaya mini.

Karanta cikakken babi Ayu 19